Isa ga babban shafi
Philippines- Korea ta Arewa

Philippine ta Kwace wani Jirgin Ruwa na Koriya ta Arewa Saboda Karya Takunkumi

Jami'an kasar Philippine sun tsare wani jirgin ruwa na  kasar Koriya ta Arewa saboda karya takunkumin hana zirga-zirga da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa kasar Koriya ta Arewan na baya-bayan nan.

Taswirar Philippines Subic
Taswirar Philippines Subic rfi
Talla

Hukumomin Philippines na cewa jirgin ruwan ba zai bar tashan ruwan Subic ba, dake arewacin Manilla inda ake tsare dashi yau kwanaki uku ke nan, tare da dukkan maaikatan jirgin ruwan.

Wannan shine karo na farko matakin da aka dauka kan Koriya ta Arewa tun bayan tsauraran takunkumi da aka kakaba mata ranar Laraba da ta gabata saboda kunnen kashi da ta nuna wajen chilla makami mai linzami.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.