Gwamnatin Philippines ta cim ma yarjejeniya da Kungiyar Musulmi
Gwamnatin kasar Philippine ta cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da shugabannin Kungiyar Musulmi ta Moro a yau Alhamis, wadanda ke tawaye da ita a wani mataki da zai kawo karshen rikicin yankin kudancin kasar da ya lakume rayukan dubban mutane.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A Fadar Shugaban kasa ne bangarorin biyu suka sa hannu ga yarjejeniyar sulhu a fadar a Manila.
Addinin Musulmi ya shiga kasar Philippines ne tun a wajajen karni na 13 saboda cudanyar kasuwanci da Larabawa.
Kungiyar ‘Yan tawayen Moro suna da mabiya sama da 10,000 masu dauke da makamai a cewar rundunar Sojin kasar Philliphines, kuma sun dade suna fafutikar kafa kasa mai cin gashin kanta a kudancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu