Isa ga babban shafi
IRAN

Shirin Nukiliyar Iran ya fuskanci tsaiko

Kasar Iran tare da kasashen da suke tattaunawa dan kulla yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka sanya gobe 30 ga wata a matsayin ranar karshe, sun ce zai yi wuya a kulla yarjejeniyar saboda wasu yan matsalloli da ke tsakanin su.

Kasashen da ke tattauna shirin Nukiliyar Iran
Kasashen da ke tattauna shirin Nukiliyar Iran REUTERS/Carlos Barria
Talla

Wakilan da ke halartar taron dai sun ce ba za su iya kamala tattaunawar gobe ba, yayin da Iran ta ke cewa babu wani shiri na tsawaita lokacin kamala tattaunawar.

Tuni ministan harkokin wajen Iran Mohammed Zarif ya koma gida dan ganawa da hukumomin kasar, yayin da Amurka ta ce babu wani abin damuwa akai, domin haka tattaunawar ta gada.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond ya ce lalle suna da kalubale sosai a gabansu wajen kulla yarjejeniyar, inda ya ke cewar shi da takwarorin sa na iya haure takalmansu su yi tafiyar su idan hakan ya zama wajibi.

Ita kuwa Babbar jami’ar diflomasiyar kasashen Turai Federico Mogherini ta ce ya zama dole kowanne bangare ya nuna manufa mai kyau dan kawo karshen tattaunawar da aka kwashe shekaru biyu ana yi.

Su dai kasashen da ke tattaunawar na bukatar ganin Iran ta ce ta rage sinadarin nukiliya, barin masu sa ido su ziyarci sansanin ta na soji da kuma daina sarrafa uranium, yayin da Iran ke bukatar ganin an sake mata kudaden ajiyar ta da ke kasahsen waje.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.