Isa ga babban shafi
Iran

An tsawaita wa’adin tattauna yarjejeniya da Iran

Iran da manyan kasashen duniya sun sake ba kansu karin wa’adi na watanni domin ci gaba da tattauna batun yarjejeniyar nukiliya da Iran bayan wa’adin da suka diba ya cika a jiya Litinin. Bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa har zuwa ranar daya ga watan Yuli.

Zauren tattaunawa tsakanin Manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya
Zauren tattaunawa tsakanin Manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

A jiya Litinin ne wa’adin da Iran da manyan kasashe suka diba domin amincewa da yarjejeniya ya kawo karshe bayan sun kasa cim ma jituwa kan wasu batutuwa da Iran.

Ministan harakokin wajen Rasha yana cikin Jami'an diflomasiyar manyan kasashen da suka halarci zaman tattaunawar a Vienna tare da Amurka da Birtaniya da China da Jamus da Faransa.

Manyan kasashen suna son Iran ta jingine shirinta na mallakar makaman nukiliya domin sassauta ma ta takunkumin da ke wuyanta.

Amma Iran na nanata cewa tana neman bunkasa makamashi ne sabanin tunanin manyan kasashen.

Iran da manyan kasashen sun bayyana fatar cim ma jituwa a tsakaninsu kafin cikar wa’adin da suka diba.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga manyan kasashen duniya akan kada su yi kuskuren amincewa da yarjejeniyar da zasu yi da na sani.

Netanyahu yace Iran na iya cim ma bukatunta na mallakar makaman Nukiliya idan har kasashen duniya suka amince da yarjejeniyar da za ta yi wa Iran dadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.