Isa ga babban shafi
Iran

Shirin Iran na Nukiliya yana nan- Zarif

Dalilan da manyan kasashen duniya ya sa suka kakabawa kasar Iran Takunkumi, sune don tursasawa kasar ta janye shirinta na Nukiliya. To sai dai Yarjejenyar da aka cim ma tsakanin bangarorin biyu a Geneva, Iran ta samu sassaucin takunkumi ba tare da dakatar da daukacin shirinta na Nukiliya ba.

Mohammad Javad Zarif Ministan harakokin wajen Iran ya rungume Laurent Fabius na Faransa
Mohammad Javad Zarif Ministan harakokin wajen Iran ya rungume Laurent Fabius na Faransa REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Iran da manyan kasashen duniya sun cim ma yarjejeniyar ne ta tsawon watanni shida bayan kwashe kwanaki biyar suna tattaunawa.

A cikin yarjejeniyar, bangarorin biyu sun amince Iran ta dan ja da baya akan shirinta na Nukiliya yayin da manyan kasashen suka amince su sassauta wa kasar jerin takunkumin da suka kakaba ma ta wanda ya gurgunta tattalin arzikin Tehran.

Wannan kuma kamar gwaji ne na tsawon watanni shida kafin manyan kasashe na duniya da ake kira P5+1 su warware da Iran.

Mista Zarif wanda ya jagoranci zaman tattaunawar a matsayin wakilin Iran yace kasashen na duniya sun fahimci hakkin ‘Iran na inganta shirinta na Uranuim sabanin tunaninsu na Nukiliya

Wannan yarjejeniyar kuma na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Hassan Rohani mai sassaucin ra’ayin ke bukin cika kwanaki 100, yayin da Jagoran kasar Ayatollah Ali Khamenei, ke bayyana cewa wannan tamkar nasara ce ga Iran.

Akwai dai jerin takunkumi da MDD ta lankaya wa Iran guda hudu ne, kamar yadda EU ta kakabawa iran takunkumin katse huldar kwasuwancin tare da rufe asusun babban bankin kasar.

Amurka kuma ta lankaya wa Iran takunkumi ne guda 7 da suka shafi haramtawa Amurkawa huldar kasuwanci da kasar wannan kuma duk saboda Shirin Iran na nukiliya.

Tuni dai Saudiya ta yi na’am da matakin yayin da kuma Isra’ila ke ci gaba da adawa inda yanzu haka ta aika da jekada zuwa Amurka domin tattaunawa akan yarjejeniyar da aka cim ma da Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.