Isa ga babban shafi
Iran

Za’a ci gaba da tattauna batun Nukiliya da Iran

Manyan kasashen duniya da ke tattauna batun nukiliya da kasar Iran sun karawa kan su lokaci na tsawon watanni hudu bayan sun kammala zaman tattaunawa a birnin Vienna ba tare da cim ma maslaha ba tsakaninsu da Iran.

Ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif tare da wakilan manyan kasashen duniya suna tattauna batun Nukiliya a Vienna
Ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif tare da wakilan manyan kasashen duniya suna tattauna batun Nukiliya a Vienna REUTERS/Jim Bourg
Talla

Babbar Jami’ar diflomasiyar Turai Catherine Ashton ta shaidawa manema labarai cewa zasu ci gaba da tattaunawa da Iran domin har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa da suke da sabani akai.

Karkashin yarjeniyar da bangarorin biyu suka cim ma, kafin tsawaita wa’adin tattaunawar, kasar Amurka ta amince ta bude asusun Iran na kudi kusan dala Miliyan uku, yayin da kuma Iran zata sauya kashi 20 na samar da makamashin Uranium da ake hada bama bamai zuwa samar da Mai.

Iran dai tana fuskantar kalubale ne daga manyan kasashen duniya masu kujerar din-din guda biyar a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.