Isa ga babban shafi
Iran-IAEA

Yarjejeniyar Nukiliya ta fara aiki a Iran

Kasar Iran ta fara dakatar da kashi 20 na ayyukan hako makamashin Uranium karkashin yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya game da shirinta na Nukiliya da suka cim ma a Geneva.

Cibiyar makamashi a kasar Iran
Cibiyar makamashi a kasar Iran Reuters/Raheb Homavandi
Talla

Hukumar makamashi ta duniya ce ta tabbatar da Iran ta fara jingine ayyukanta na Uranium karkashin yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen Duniya guda shida Amurka da China da Rasha da Faransa da Bitaniya da kuma Jamus.

Babban Jami’in hukumar Makamashi ta Iran Mohammad Amiri, yace a gaban wakilan Majalisar Dinki Duniya ne suka dakatar da ayyukan Uranium a cibiyar Natanz da Fordo.

Karkashin yarjejeniyar, akwai jerin Takunkumi da manyan kasashen zasu sassautawa kasar Iran tare da rage fargabar yaki da Amurka da Isra’ila ke barazanar yi da kasar Iran.

Yanzu dai nan da makwanni shida masu zuwa Iran ba zata sake dasa wasu sabbin na’urori ba tare da ba wakilan hukumar Makamashi damar shiga cibiyoyin sarrafa makamashi da aka rufe a ko da yaushe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.