Isa ga babban shafi
Iran

Majalisar Iran ba za ta yanke hukunci na karshe ba gameda yarjejeniyar aikin nukiliya

Majalisar Dokokin kasar Iran ta rage karfin da take dashi gameda hana aiwatar da yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya shida saboda zargin aikin nukiliya da mugun nufi.  

Wata ganawa da Sakataren wajen na Amirka John Kerry ya yi da wakilin Iran gameda batun nukiliya Mohammed Javad Zarif ranar  16/03/2015.
Wata ganawa da Sakataren wajen na Amirka John Kerry ya yi da wakilin Iran gameda batun nukiliya Mohammed Javad Zarif ranar 16/03/2015. Reuters
Talla

A ranar 30 ga wannan wata ne wa'adfin yarjejeniya tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya shida zai cika saboda a sasanta ko kasar ta sami sassaucin takunkumin da aka malkaya mata.

Daftarin dokan da majalisar ta gabatar Laraba data gabata wanda ya bullo da wasu tsauraran sharudda kafin kasar ta amince da wata yarjejeniya da manyan kasashen duniyan, ya nemi kawo cikas ga yarjejeniyar.

Sai dai kuma yanzu haka a wani mataki da ake ganin karin karfin guiwa ne ga Shugaba Hassan Rouhani, yanzu  batun amincewa da yarjejeniyar harkan nukiliyan da manyan kasashen shida baya hannun wakilan majalisar Dokokin.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.