Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya lashe zaben Shugaban kasar Amurka wa'adi na biyu

Shugaban Amurka Barack Obama ya lashe zaben Shugaban kasa wa’adi na biyu bayan samun kuri’u mafi rinjaye a jahohin Ohio da Wisconsin wanda ya ba shi damar doke Mitt Romney na jam’iyyar Republican. Tuni dai Mitt Romney ya taya Obama Murna ta wayar Salula tare da amsa shan kaye.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama Reuters/Jim Bourg
Talla

“ Wasu Shekaru Hudu” kalaman da Obama ya yada ke nan a shafin shi na Twitter a Intanet.

Barack Obama ya samu yawan kuri’u 270 da ake bukata wanda shi ne shugaban Amurka bakar fata na farko a Tarihin Amurka.

Obama dai ya lashe zaben ne duk da kalubalen matsalar tattalin arzikin da ya fuskanta daga abokin hamayyar shi Mitt Romney.

Obama ya lashe kuri’u 303 yayin da Mista Romney ya samu yawan kuri’u 203.

A birnin Boston hedikwatar Yakin neman zaben Romney, Dan takar ya mika sakon taya murna ga abokin hamayyar shi Barack Obama.

A tsarin zaben Amurka karkashin kundin tsarin mulkin kasar, ko wace Jaha akwai adadin kuri’unta ta la’akari da yawan mutanen Jahar.

Yanzu haka Barack Obama ya shiga tarihin Jam’iyyar Democrat a matsayin shugaba na biyu da ya samu nasarar yin Tazarce tun bayan kawo karshen yakin duniya na Biyu. Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton wanda shi ne jagoran yakin neman Zaben Obama a shekarar 1996 ne ya lashe zaben shugaban kasa wa’adi na biyu karkashin Jam’iyyar Democrat.

Barack Obama shi ne Shugaba na 44, a jerin shugabannin kasar Amurka, kuma bakar fata na Farko da ya shiga fadar White House.

Tuni shugaban ya aike da sakon godiya ga magoya bayan shi, ta shafin zumunta na Twitter, yana mai godiya ga magoya bayan shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.