Isa ga babban shafi
Amurka

‘Yan kasar China da Japan sun goyi bayan Obama ya yi Tazarce

Wani zaben ra’ayin Jama’a da kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP ya gudanar kafin kada kuri’ar zaben shugaban Amurka, sakamakon zaben ya nuna ‘Yan kasar China da Japan suna goyon bayan Barack Obama ya yi tazarce wa’adi na biyu, binciken kuma yace tsauraran kalaman da Mitt Romney ya furta game da karfin ikon Yankin Asiya ya rage masa kima.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama a lokacin da ya ke yakin neman zabe
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama a lokacin da ya ke yakin neman zabe REUTERS/Larry Downing
Talla

Binciken ya nuna kashi 83 na ‘yan kasar Japan sun bayyana nuna goyon bayansu ga Barack Obama inda kashi 12.3 suka ce Mitt Romney ne dan takararsu.

‘Yan kasar China kuma kashi 63 ne suka ce suna Bukatar Obama ya sake shugabantar Amurka a wa’adi na biyu. An gudanar  zaben ra’ayin Jama’ar ne a Hong Kong tsakanin watan Satumba zuwa Oktoba.

Masu sharhi dai suna ganin kalaman Mitt Romney game da mamayar kudin China da tattalin arzikin Japan ya rage masa kima ga al’ummar kasashen.

Shugaba Obama dai ya sake samun kwarin gwiwa daga fitattciyar Mujallar nan da ke sa ido kan tattalin arzikin duniya, mai suna “The Economist” ta Birtaniya, inda mujallar ta yi sharhi cewa gara shugaba Barack Obama da mai adawa da shi.

A nasa bangaren kuma Magajin Garin Birnin New York, Michael Bloomberg, mai fada aji a cikin kasar Amurka, yace duk da matsalolin da aka samu a cikin kasar, gara shugaban ya samu wa’adi na biyu, maimakon abokin takararsa, Mitt Romney.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.