Isa ga babban shafi
Amurka

Obama da Romney sun yi musayar kalamu akan manufofin wajen Amurka

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya soki abokin karawar shi Mith Romney game da batutuwan da suka shafi manufofin harakokin wajen Amurka a muhawarar karshe da suka tabka kafin a jefa kuri’ar zaben shugaban kasa nan da makwanni biyu.

Shugaba Barack Obama na Demokrat da Mitt Romney na Republican a lokacin da suke tabka muhawara ta karshe
Shugaba Barack Obama na Demokrat da Mitt Romney na Republican a lokacin da suke tabka muhawara ta karshe REUTERS/Rick Wilking
Talla

A muhawarar dai Mith Romney ya yi kokarin sukar Obama wajen gurgunta tattalin arziki da matsalar rashin aikin yi da kuma matsalar ba shi da ke ci gaba da karuwa.
Mista Romney yace Obama ya taka rawa wajen gurguncewar yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.

A lokacin muhawar ‘Yan takarar biyu sun yi musayar kalamai game da zanga-zangar kasashen Larabawa da matsalar Nukiliyar Iran da rikicin Isra’ila da kuma jayayyar da Amurka ke yi da China a mamayar tattalin arzikin duniya.

Shugaba Barrack Obama, yace kungiyoyin ‘Yan ta’adda ne za su ci gaba da zama barazana ga Amurka a shekaru masu zuwa. Shugaban kuma yace sun samu gagarumar nasara a manufofinsu na kasashen waje tare da sukar Mitt Romney idan aka ba shi damar shugabanci, zai mayar da kasar baya da manufofinsa na rashin kwarewa a fannin Diflomasiya.

Sakamakon muhawarar dai ya nuna Obama ya samu kuri’u kashi 50 a matsayin wanda ya lashe muhawar ta karshe amma Romney ya samu kuri’u kashi 23 yayin da kuma kashi 24 suka ce an yi kunnen doki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.