Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben Amurka: An tabka muhawara tsakanin Biden da Ryan

Masu neman kujerar mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden na Democrat da Paul Ryan na Republican sun fafata a muhawarar da aka gudanar tsakaninsu domin samun goyon bayan Amurkawa a zaben 6 ga watan Nuwamba. ‘Yan takarar biyu sun yi musayar kalamai ne akan batun tsaron kasa da tattalin arziki da haraji da kuma tsarin kiyon Lafiya.

Paul Ryan, na Republican da  Joe Biden, na Democrat a lokacin da suke tabka muhawara
Paul Ryan, na Republican da Joe Biden, na Democrat a lokacin da suke tabka muhawara REUTERS/Mike Segar (L)/Jason Reed (R)
Talla

Mataimakin shugaban kasa mai ci Joe Biden ya yi kokarin kare Shugaba Barack Obama tare da farfado da darajar Jam’iyyar Demorat bayan Obama ya sha kaye a muhawar farko da aka gudanar tsakanin shi da Mitt Romney.

Sai dai duk da wannan ci gaban, masu lura da Siyasar Amurka suna ganin idan Obama yana fatar ganin ya lashe zabe wa’adi na biyu, dole sai ya yi kokarin kare kansa a muhawara da za su fafata nan gaba.

Samun nasarar Obama a zaben da za’a gudanar ya samu rashin tabbas, bayan da dan takarar shugabancin kasar, karkashin tutar Republican Mitt Romney ya sha gaban shi tsawon mintoci 90 a muhararar da suka tabka a ranar uku ga watan Oktoba, al’amarin da ya sa tagomashin shugaban ya ragu a idon Amurkawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.