Isa ga babban shafi
Amurka

Jam’iyyar Republican ta tsayar da Romney a matsayin Dan takara

Jam’iyyar adawa ta Republican a Amurka ta tsayar da Mitt Romney a matsayin dan takarta wanda zai kara da Shugaba Barrack Obama a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Nuwamba. Ann Uwargidan Romney tace Mijinta ba zai ba Jam’iyyar Republican kunya ba.

Mitt Romney Dan takarar Jam'iyyar Republican tare da matarsa  Ann à Tampa, Jahar  Florida
Mitt Romney Dan takarar Jam'iyyar Republican tare da matarsa Ann à Tampa, Jahar Florida REUTERS/Jason Reed
Talla

Mitt Romney shi ne dan takarar da ya samu rinjayen kuri’u Bayan kammala zaben fitar da gwani a Jahohin Amurka, Romney ya samu adadin kuri’un da ake bukata kafin tsayar da Dan takara domin ya samu goyon bayan wakilan Jam’iyyar 1,144.

Romney mai shekaru 65 na haihuwa kuma attajirin dan kasuwa, a gobe Alhamis ne zai gabatar da jawabin amincewa da jagorantar Jam’iyyar Republican a zaben shugaban kasa a Tampa Jahar Florida.

Wani sakamakon zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna Romney yana kafada da kafada ne da Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.