Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya mayar wa Romney da martani a muhawarsu ta biyu

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kare kansa tare da mayar wa Mitt Romney dan takarar Jam’iyyar Republican da martani a muharawar da suka gudanar karo na biyu kafin zabe. Obama ya tabo bututuwan da suka shafi tattalin arziki da haraji da diflomasiya amma Romney yace akwai gazawa ga Gwamnatin Obama.

Barack Obama da  Mitt Romney, a lokacin da suke tabka Muhawara
Barack Obama da Mitt Romney, a lokacin da suke tabka Muhawara
Talla

A muharar farko da aka gudanar ana kallon Mitt Romney ya kayar da Obama amma a karawa ta biyu masana suna ganin Obama ya sanya ruwan sanyi ga magoya bayan Jam’iyyarsa ta Democrat.

A kokarin Obama na yin tazarce, sai ya yi kokarin samun goyon bayan Jahohi Tara da ake tunanin za su ba shi damar lashe zaben da za’a gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamba.

An gudanar da Muhawar ne a Jami’ar Hofstra, kuma ‘Yan takarar biyu sun yi musayar kalamai tare da sukar juna na tsawon Minitina 90.

Mitt Romney dai ya zargi Barack Obama da soke lasisin gidaje da kamfanoni, abinda ya sa mutane da dama suka rasa aiki da samun kudin shiga. Amma kuma Obama ya kare kansa.

00:42

Dakta Ibrahim Khalil, malami a Jami’a Missouri

Bashir Ibrahim Idris

Bayan zarginsa da rashin daukar matakin kare Jakadun Amurka a Libya, Shugaba Barack Obama, ya dauki alhakin harin da aka kai ofishin Jakadancin kasar a Benghazi, wanda ya yi sanadiyar kashe Jakadan Amurka da jami’ansa.

Yayin da ya ke jawabi Obama yace Hillary Clinton ta yi kokari a matsayin mai yi masa aiki, amma shi ne shugaban kasa.

Dakta Ibrahim Khalil, malami a Jami’a Missouri a kasar Amurka, yace da Farko Obama bai yi tunanin Romney zai canza kalamansa ba.

07:01

Maryam Muhammed 'Yar Najeriya a Los Angeles

Bashir Ibrahim Idris

Magoya Bayan Shugaba Barack Obama sun bayyana farin cikinsu da rawar da shugaban ya taka, a mahawarar da aka gudanar karo na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.