Isa ga babban shafi
Amurka

Amurkawa sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa

An bude rumfunan zabe a Kasar Amurka a yau Talata domin bawa Amurkawa dama su zabi tsakanin shugaba Barack Obama na Jami’iyar Democrat ko kuma tsohon Gwamnan Jihar Massachusetts, Mitt Romney, wanda zai yi takara a karkashin jam’iyar Republican. Obama, dan shekau 51, da Romney dan shekaru 65 na tafiya ne kankankan a kuri’ar da aka gudanar na jin ra’ayoyin mutane game da wanda ake ganin zai lashe zaben.  

Rumfunan zabe a kasar Amurka
Rumfunan zabe a kasar Amurka REUTERS/Matt Sullivan
Talla

A jiya ne 'Yan takarara biyu suka shiga ranar karshe a yakin neman zabensu, inda yanzu haka hankulan mutane ya koma kan wasu jihohi 10 da ake sa ran zasu raba gardama tskanin Obama da Romney in da suka kwashe daren Lahadi suna yakin neman zabe a sassan yankunan Amurka.

Obama ya kwashe daren Lahadi yana yakin neman zabe a Jahohin New Hampshire da Florida da Ohio da Colorado inda kuma Romney ya hada gangami a Pennsylvania.

Mista Obama da Mista Romney suna ta fiya kafada kafada ne a zaben ra’ayin jama’a da aka gudanar kafin zaben, amma sakamakon zaben na nuna Obama ne akan gaba.

Barack Obama, yana fatar janye hankalun masu zabe a Jihohi 10 masu masana’antu saboda rawar da ya taka, wajen ceto wasu kanfanonin jahohin, yayin da magoya bayan Mitt Romney ke cewar, sune a kan gaba a wadannan Jihohi, saboda yadda jama’arsu ke neman sauyi.

Hasashe na nuna cewa, muddin shugaba Obama ya samu nasarar lashe Jihohin Ohio, Winsconsin da Iowa, to babu abinda zai hana shi samun nasarar zaben, abinda zai ba shi damar zama shugaban Democrat na biyu da zai sake lashe zaben wa’adi na biyu.

Jihohi 10 da zasu tantance sakamakon zaben Amurka sun hada da Pennsylvania da Michigan da Minnesota da Nevada da Colorado da New Hamshire da Virginia da Winsconsin da Ohio da Florida, wadanda ke da matukar tasiri ga ‘Yan takarar Amurka. kuma rahotanni sun ce Obama na kan gaba a a kasarin wadannan Jihohi.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton, wanda har yanzu yana da karfin fada aji a kasar, ya sake jaddada goyan bayansa ga Barack Obama, inda ya bukaci ‘Yan kasar su ba shi damar ci gaba da kokarinsa na ceto kasar daga halin da ‘Yan Jam’iyar Republican suka jefa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.