Isa ga babban shafi
Amurka-Afrika

Martabar Obama ga idon al’ummar Afrika

Shekaru hudu da suka gabata, Al’ummar Afrika sun yi murna matuka bayan zaben Barck Obama a matsayin shugaban Amurka, domin tunanin shugaban Amurka bakar fata na farko zai kawo ci gaba ga al’ummar Nahiyar, amma kuma labarin ba haka ba ne a shekaru hudu da Obama ya kwashe yana shugabancin Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Bayan zaben shi a shekarar 2008, Nelson Mandela na Afrika ta Kudu da Ministan harakokin wajen Najeriya suna cikin wadanda suka zubar da hawaye saboda murna.
A kasar Kenya, kuma Tushen Obama gwamnatin kasar ta ware rana ne a matsayin hutu.

Obama ya yi kokarin kawo karshen yakin Iraqi da Afganistan amma wasu kasashen Afrika musamman yankin Sahara sun samu kansu ne cikin yaki a zamanin mulkin Obama.

Mutane da dama sun yi tsammanin Obama zai kasance shugaban Amurka don Afrika. Amma wani jami’in Diplomasiyar Afrika ta Kudu Thomas Wheeler yace ba lalle ba ne Obama ya tsinanawa Afrika wani abu ba.

Yanzu haka wasu kasashen Afrika sun rikde sun koma kamar kasashen Gabas ta tsakiya inda ake zubar da jini, kasashe irinsu Somalia da Mali da Congo da Najeriya da zanga zangar kasashen Arewacin Afika da shafi Libya da Masar da Tunisia.

Sai dai kuma tun lokacin da Obama ya karbi ragamar shugabancin Amurka akwai Rahotanni da ke cewa ya aiko da ‘Yan leken asiri wadanda ke buya a kasashen Burkina Faso da Uganda domin farautar ‘Yan kungiyar Al Qaeda reshen Magrib da ‘Yan tawayen Congo na Lord Resistance Army.

A bana dai zaben Obama ba shi ne damuwar al’ummar Afrika ba, domin halin tabarbarewar matsalar tsaro shi ne ya dame su, domin akwai rikicin Boko Haram a Najeriya, da rikicin ‘Yan tawayen mali da ke barazana ga kasashen da ke makwabtaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.