Isa ga babban shafi
Amurka

Likitocin Amurka zasu tantance kwayar rage kiba da aka samar

Hukumar tantance magani a kasar Amurka zata yanke hukunci a watan Yuli game da kwayar magani ta Qnexa da za’a sha a rage kiba. Wanda kamfanin samar da kwayar magani na VIVUS ya samar.

Wasu masu fama da Kiba a gida daya a kasar Amurka
Wasu masu fama da Kiba a gida daya a kasar Amurka
Talla

A Ranar 17 ga watan Yuli ne aka tsayar a matsayin ranar da za’a kaddamar da maganin Qnexa bayan an dauki dogon lokaci ana mahawara game da fitar da kwayar maganin a kasuwa saboda wasu illolin da maganin kan iya haifarwa ga mata masu juna biyu da wandanda suka sha Maganin ba bisa ka’ida ba.

Tun a shekarar 2010 hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka ta dakatar da fitowar kwayar maganin don tabbatar da ingancinsa da yadda za’a kiyaye bayan kamfanin ya bayyana illar da maganin zai haifar idan aka saba ka’idan shan sa.

Bincike da aka gudanar ya nuna maganin Qnexa ya kunshi karfin magungunan rage kiba biyu da zai rage kashi Goma na kibar mutum cikin kankani lokaci. Idan mutum yana motsa jiki tare da cin lafiyyen abinci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.