Shirin Lafiya Jari ya diba matsalar hunturu ga Lafiyar al'umma a kasashen Afrika tare da tattaunawa da Likita wanda ya yi bayani dangane da yadda mutum zai kare lafiyar shi ga kamuwa da cutar Asma.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance
Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance06/05/202410:09 -
Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai.03/05/202410:07 -
Yadda maza a Najeriya ba sa bai wa gwajin sankarar mafitsara mahimmanci
A wannan mako shirin ya mayar da hankali kan nau’ikan cutakan da ba a fiya mayar da hankali wajen yakarsu ba musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wannan nau’in cutuka kuwa sun kunshi kansar mafitsara ko kuma Prostate Cancer, nau’in kansar da ke matsayin mafi hadari ga maza, amma kuma ba ta samun kula duk da yadda ta ke kisan akalla mutum dubu 8 duk shekara a Najeriya.04/03/202410:00 -
Yawaitar gurbatattun jami'an lafiya a asibitocin Najeriya
A wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yawaitar gurbatattun jami’an lafiya a asibitocin Najeriya wanda ke da nasaba da kodai rashin samun cikakken horo a kwalejojin lafiya ko kuma samun horon irin wadannan makarantu amma na bogi.A baya-bayan nan ana yawan ganin yadda ake bude tarin makarantu masu zaman kansu a sassan Najeriya da sunan horar da jami’an lafiya kama daga kwalejoji har da jami’o’I wadanda wasu daga cikinsu kan rasa sahalewar mahukuntan saboda rashin cancanta.29/01/202410:10 -
Najeriya ta fara amfani da fasahar tiyata ba tare da tsaga jiki ba
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan ci gaban da aka samu na fara amfani da fasahar fida ba tare da tsaga jikin majinyaci ba a Najeriya, a wani yunkuri na rage dogaro da kasashen ketare wajen irin wannan fida.18/12/202309:59