Isa ga babban shafi
EU-Girka-IMF

IMF ta amince da sabon bashin kasar Girka

Hukumar Bada lamuni ta Duniya, ta amince da sabbin Karin rance ga kasar Girka, a wani yunkurin irin na kasashen Turai, don ceto kasar daga matsalar basuka. Kwamitin zartarwar hukumar ya bada umurnin bai wa kasar Girka bashin kudi euro Biliyan 28 domin samun kwarin gwiwar ci gaba da aiwatar da tsarin tsuke bakin aljihu.

ministan kudin kasar Girka Evangelos Venizelos tare da Fira ministan kasar girka Lucas Papedemos a lokacin da suke ganawa da manema labari a Brussells
ministan kudin kasar Girka Evangelos Venizelos tare da Fira ministan kasar girka Lucas Papedemos a lokacin da suke ganawa da manema labari a Brussells REUTERS/Yves Herman
Talla

Hukumomin Bankin sun amince da shirin bai wa Girka rancen Dala biliyan 28, don aiwatar da shirin tsuke bakin aljihu, kamar yadda shugabar Hukumar, Christine Lagarde tace sun gamsu da matakan da kasar ke dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.