Isa ga babban shafi
Girka

Majalisar Kasar Girka ta amince da rage kasafin kudi

Majalisar dokokin kasar Girka, ta amince da sabon shirin rage kasafin kudin kasar, sakamakon yarjejeniyar tallafin kungiyar kasashen Turai.Yan Majalisun kasar sun yi watsi da Jam’iyyun su, inda suka amince da zabtare Dala bilyan 3, da miliyan 200 daga kasafin kudin. 

Reuters/Yiorgos Karahalis
Talla

Kungiyoyin kwagadon kasar sun kalubalanci matakan tare da kirar tsayar da aiyuka na tsawon sa'oi uku. Gamayyar kungiyoyin kwadogon kasar sun kuma shirya zanga zanga a tsakiyar Athens babban birnin kasar ta Girka.

Kasar ta ci gaba da daukan matakan tsuke bakin aljuhu, tare da samun tallafi daga kungiyar kasashen Tarayyar Turai, inda ake neman hanyoyin sake daidaita tattalin arzikin kasar.

Fira Ministan kasar ta Girka Lucas Papademos zai gana da shugaban kwamitin Tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.