Ministocin Turai sun amince da yarjejeniyar tallafawa Girka
Ministocin Kudaden kasashen Turai sun amince da yarjejeniyar bayar da Tallafin kudi euro biliyan 130 ga kasar Girka, bayan kwashe daren jiya suna tafka mahawara. Yarjejeniyar ta kunshi yafewa Girka bashin da hukumomin kudade ke bin ta na sama da kashi 53, da kuma wasu euro biliyan 100 daga biliyan 350 da ake bin ta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Fira ministan kasar Girka Lucas Papademos ya bayyana jin dadisa game da jyarjejeniyar bada Tallafin da aka cim ma
Yanzu haka kuma darajar kudin euro ta haura sama bayan samun labarin cim ma yarjejeniyar Tallafawa kasar Girka.
Sai dai Shugban Bankin Turai, Jean Claude Juncker yace zasu karfafa wa kwamitin da zai sa ido ga kasar Girka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu