Isa ga babban shafi

jam'iyyar adawa ta Burundi ta samu rarrabuwar kawuna

Babbar jam'iyyar adawa ta Burundi ta samu rarrabuwar kawuna a yau Lahadi bayan da wani bangare ya ce sun hambarar da shugabanta Agathon Rwasa saboda gazawar bangarorin biyu.

Agathon Rwasa, Shugaban yan Adawa na Burundi
Agathon Rwasa, Shugaban yan Adawa na Burundi © ONESPHORE NIBIGIRA / AFP
Talla

Yan jam’iyyar adawa ta kasar ta Burundi sun tsige Rwasa ne daga matsayin shugaban hukumar 'yancin walwala ta kasa (CNL) da aka dakatar a babban taron da aka yi a arewacin kasar, kamar yadda majiyoyi da shaidun  suka tabbatar.

An maye gurbin tsohon shugaban ‘yan tawayen ne mai shekaru 60 da Nestor Girukwishakae, babban jami’in gudanarwa a wani kamfani mallakar gwamnati.

Masu sukar lamirin sun ce matakin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta dauka wani yunkuri ne na murkushe 'yan adawa gabanin zaben 'yan majalisar dokoki na shekara ta 2025 da kuma kasadar mayar da kasar cikin rudanin siyasa.

Shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye,
Shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye, AP - Brian Inganga

Sakataren jam’iyyar Simon Bizimungu ya yi tir da tsige Rwasa, yana mai cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkinsu.

Bizimungu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa "Wannan ya sabawa doka ta 47 na dokokin jam'iyyar, wadda ta ce shugaban kasa da halaltaccen lauya ne kadai ke da ikon gudanar da irin wannan taro."

Agathon Rwasa, Shugaban yan adawa na Burundi
Agathon Rwasa, Shugaban yan adawa na Burundi © ONESPHORE NIBIGIRA / AFP

Bizimungu ya zargi ministan cikin gida Martin Niteretse da kin bai wa Rwasa damar gudanar da babban taro na kansa a ranar 2 ga Maris, amma "ya ba da izini ga wasu tsirarun gungun 'yan adawa 10 da su shirya taron a nasu bangaren.

Wani babban jami'in CNL ya ce dole ne 'yan majalisar masu adawa da gwamnati su mika shawarwarin taron na ranar Lahadi ga ma'aikatar cikin gida da nufin samun amincewar ta.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa taron na ranar Lahadi ya gudana ne a karkashin dimbin ‘yan sanda.

Rwasa ya zo na biyu bayan Shugaba Evariste Ndayishimiye a zaben 2020, wanda 'yan adawa suka ce ba shi da kura-kurai.

Shugaba Evariste Ndayishimiye ya kasa inganta yanayin hakkin dan Adam na muni kuma kasar mai mutane miliyan 12 ta kasance daya daga cikin mafi talauci a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.