Isa ga babban shafi

Gwamnatin Burundi ta zargi kunfitar yan tawayen RED-Tabara da kashe akalla fararen hula 20

Shugaban Burundi Évariste Ndayishimiye
Shugaban Burundi Évariste Ndayishimiye AFP
Talla

Akalla mutane 20 ne da suka hada da 19 farar hula aka kashe  a yankin yammacin kasar Burundi, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar, harin da gungun mayakan yan tawayen RED-Tabara suka dau nauyi, duk da cewa,  su a sun ce sojojin gwamnati 10 ne suka kashe

An kai harin ne a ranar juma’ar da ta gabata a kauyen Vugizo, mai tazarar kilo mita sama da 20 da Bujumbura babban birnin cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar, da kuma ya hada iyaka da kasar Jamhuriyar Demkradiyar Congo (JDC), kasar da a cikinta sansanin cibiyar yan tawayen na  RED-Tabara (Résistance pour un État de Droit au Burundi), babbar kungiyar yan tawayen da ke yakar gwamnatin da Evariste Ndayishimiye ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.