Isa ga babban shafi

An yanke wa tsohon Firaministan Burundi hukuncin daurin rai-da-rai

Kotu a Burundi ta yankewa tsohon Firaministan Kasar Alain-Guillaume Bunyoni hukuncin zaman din-din-din a gidan kas, bayan kama shi da laifin yunkunrin juyin Mulki, wawure dukiyar Kasa, tare da gurguntar da tattalin arzikin Kasar ta Burundi.

Tsohon Firaministan Burundi
Tsohon Firaministan Burundi © AFP
Talla

A cikin watan Yulin shekarar 2020 aka rantsar da Alain-Guillaume Bunyoni mai shekaru 51 a duniya, a matsayin firaministan Kasar, saidai bayan shekara biyu da samun matsayin aka kore shi, cikin watan satumban shekarar 2022.

Korar Bunyoni na zuwa ne kwanaki 2 bayan shugaban KasarEvariste Ndayishimiye ya yi gargadi game da yunkurin samun juyin Mulki a Kasar.

Hukuncin da aka yankewa tsohon firaministan ya kuma hada da kwace wasu daga cikin kadarorinsa da suka hada da gidaje 4, da fili da kuma motoci 14. Haka ma akwai wasu muarrabansa 5, cikinsu har da babban jami’in dan sanda, da wani babban jami’in sirri, wadanda aka yankewa hukuncin zaman gidan kaso tsakanin shekara 3 zuwa 15.

Shi dai Firaministan Burundi Alain-Guillaume Bunyoni da ya kasance makusanci ga tsohon shugaban Kasar Burundi, Pierre Nkurunziza, ya taka rawar gani a jam’iyya mai ci ta CNDD-FDD.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.