Isa ga babban shafi

Kotu a Masar ta yankewa wasu manyan 'yan adawar kasar hukuncin kisa

Kotun Koli da gwamnatin Masar ta kafa musamman don hukunta manyan laifukan da suka shafi tsaron kasa ta yankewa manyan jagororin kungiyar yan uwa musulmi hukuncin kisa sakamakon samun su da hannu kan tayar da rikicin 2013 da yayi sanadin hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

Shugaban kasar Masar, Abdel-Fattah el-Sissi kenan.
Shugaban kasar Masar, Abdel-Fattah el-Sissi kenan. AP - Amr Nabil
Talla

Cikin mutanen da aka yankewa hukuncin har da babban kwamandan kungiyar Muhammad Badie.

Badie shine kwamandan kungiyar na 8 da ya jagoranceta daga 2010 zuwa 2013, kuma an kama shi ne dai-dai lokacin da sojoji suka karbe iko daga hannun Morsi.

Bayanai sun nuna wasu daga cikin wadanda aka yanke musu hukuncin kisan na yau, an yanke musu hukunce-hukuncen kisa a wasu laifukan da aka kama su da su a baya.

A wannan karon an zargi mutanen da sake hada kai wajen kulla yadda za’a kifar da gwamnatin Abedlfattah Al-sisi, wanda shima din ya karbi shugabancin kasar ne ta hanyar juyin mulki, sannan kuma an zarge su da kisan jami’an ‘yan sanda da lalata kayayyakin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.