Isa ga babban shafi

Masar ta yanke wa mutane 38 hukuncin daurin rai da rai saboda zanga-zanga

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutane 38 ciki har da wani dan kasuwa mai gudun hijira wanda wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta suka taimaka wajen haifar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Shugaban kasar Masar Abdel Fatah Al-sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fatah Al-sisi © AP
Talla

Ba kasafai ake gudanar da zanga-zangar ba a kasar Masar, sakamakon yadda shugaba Abdel Fattah el-Sissi ya ke murkushe 'yan adawa. Sai dai jerin wasu faifan bidiyo da dan kasuwar dan asalin kasar Masar Mohamed Ali, wanda yanzu ke zaune a kasar Spain, ya wallafa a wasu shafukan sada zumunta sun haifar zanga-zangar a watan Satumban 2019 saboda zargin cin hanci da rashawa da sauran batutuwa.

23 daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai an yi musu shari'a ba sa nan, ciki har da Ali, kamar yadda wata kotun hukunta manyan laifuka ta Masar da ke kula da shari'o'in da ke da alaka da ta'addanci ta bayyana.

Kotun ta kuma yanke wa wasu mutane 44 da suka hada da kananan yara hukuncin daurin shekaru biyar zuwa 15 a gidan yari kan laifukan. An sallami 21 daga cikin wadanda ake zargin, a cewar lauya mai kare Ossama Badawi.

Wadanda aka yanke wa hukuncin dai an same su ne da wasu tuhume-tuhume da suka hada da tada tarzoma a kan jami’an tsaro da cibiyoyin gwamnati. Lamarin ya samo asali ne daga zanga-zangar 2019 a birnin Suez mai tashar jiragen ruwa da ke bakin gabar tekun Suez.

Hukumomi sun kame daruruwan mutane a lokacin a birnin Alkahira da wasu biranen kasar. An saki da yawa amma wasu an mika su ga kotu.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha sukar irin wannan hukunci na Masar tare da yin kira ga hukumomi da su tabbatar da yin adalci a shari'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.