Isa ga babban shafi

Iyalan wadanda harin ta'addancin ya shafa a Mozambique sun gurfanar da Total

Iyalan mutanen da suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kasar Mozambique sun maka katafaren kamfanin makamashi na TotalEnergies a gaban kotu sakamakon zargin kamfanin da sakaci wajen bai wa ma’aikatan sa kariya, har ta kai ga an kai musu mummunan harin da ya hallaka mutane da dama. 

Tankin adana mai na kamfanin Total Energy na kasar Faranasa a kasar Rasha
Tankin adana mai na kamfanin Total Energy na kasar Faranasa a kasar Rasha AP - Jan Woitas
Talla

 

Iyalan wadanda suka mutu sanadin harin da kuma wadanda suka jikkata, na bukatar kotu ta tilastawa kamfanin biyansu diyya, kan zargin sa da sakaci wajen basu kariya, dalilin da ya yi ajalin ma’aikata da dama. 

Tuni dai kamfanin ya musanta zargin ya na mai cewa sam tuhume-tuhumensu basu da tushe ballantana makama. 

Harin ta'addanci

A 2021 ne ‘yan ta’adda suka farwa kamfanin dake aiki a kasar Mozambique tare da Harbin kan mai uwa da wabi, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. 

Masu shigar da karar da suka hadar da ‘yan uwan wasu mamata hudu da kuma wasu da suka tsira da munanan raunuka su uku, sun shaidawa kotun cewa kamfanin ya samu bayanan sirri kan cewa za’a kai masa hari, amma ya ki bai wa ma’aikatan kariya, ya ki basu wannan bayani don su kare kansu, har sai da aka kai harin.  

Kisan kai da gangan

Bayan da aka kai harin kuma wani karamin jirgin kamfanin ya fara aikin diban marasa lafiya, amma mai ya kare, kuma mahukuntan kamfanin wanda aikin sa shine sarrafa mai, suka ki bada izinin zuba mai a jirgin, jan kafar da ya kara yin ajalin wasu da dama, don hana mutanen ke zargin kamfanin da aikata kisan kai a fakaice. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.