Isa ga babban shafi
Faransa-Iraqi

Iraqi ta bukaci kamfanin Total katse hulda da yankin Kurdistan

Kasar Iraki ta ba kamfanin Mai na Total da ke kasar Faransa wa’adin yanke dukkan dangantaka tsakanin shi da yankin Kurdistan mai cin gashin kansa da ke Arewacin kasar .

Kamfanin  hakar Mai na Total
Kamfanin hakar Mai na Total REUTERS/Total E&P/Handout
Talla

Mukaddashin Firaministan kasar Iraqi mai kula da sha’anin makamashi Hussein Shahristani wanda ya gabatar da bukatar Hukumomin kasar yace Gwamnatin Iraqi taba da niyyar bayar da wasu kwangiloli ga kamfanonin kasashen waje.

Mukaddashin bai zayyana lokacin da wa’adin zai cika ba.

A ranar 31 ga watan Yuli Kamfanin Total yace ya sanya hannu cikin yarjejeniyar kwangila a yankin Kurdistan, wanda bai yi wa Gwamnatin kasar Iraqi dadi ba.

Kamfanin Total ya amsa cewa ya sanya hannu domin jigilar mai a yankin, amma kuma Hukumomin kasar Iraqi sun shaida masu yin haka ya saba dokokin kasar.

Filayen man da ake zance dai, suna da danyen mai ganga Biliyan Hudu, kuma a watan jiya aka fara kwalfan man, da ake ganin nan da shekaru biyar, duk rana za’a kwashi ganga dubu 535.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.