Isa ga babban shafi

Kamfanin Total ya yi biris da takunkuman kasashen yamma kan Rasha

Katafaren Kamfanin makamashi na Total da ke Faransa ya ce ba zai iya dakatar da sayan iskar gas daga Rasha ba sakamakon mamayar da kasar ta yiwa Ukraine, domin daukar matakin zai durkusar da tattalin arzikin nahiyar Turai.

Harabar katafaren ginin Kamfanin Total a wajen Paris, babban birnin kasar Faransa.
Harabar katafaren ginin Kamfanin Total a wajen Paris, babban birnin kasar Faransa. AFP - CHRISTOPHE ARCHAMBAULT
Talla

Shugaban kamfanin man Total Patrick Pouyanne wanda ya bayyana shirin kawo karshen cinikin makamashin daga Rasha nan da karshen wannan shekaran nan, ya ce daukar matakin zai baiwa Rasha damar samun biliyoyin daloli daga masu zuba jari a kasar.

Pouyanne ya ce ya san hanyar maye gurbin man fetur da dizil daga Rasha, amma kuma bai san hanyar maye gurbin iskar gas din kasar ba, ganin yadda kamfanoni suka dogara da shi domin samar da makamashin da suke amfani a injunan su.

Shugaban kamfanin ya ce babu wata hanyar maye gurbin iskar gas din dake fitowa daga Rasha, kuma yanzu haka ya sanya hannu akan kwangilar shekaru 25 wadda babu hanyar fita daga ciki.

Pouyanne ya ce muddin kasashen Turai basu sanyawa iskar gas din Rasha takunkumi ba, abinda zai sanya su ficewa daga kwangilar da suka kulla yana da wahala sosai.

Shugaban Total ya ce kamfanin ya zuba jarin da ya kai kusan Dala biliyan 13 da ake amfani da shi wajen gudanar da aiki, kuma janyewa daga kwangilar zai nuna cewar kamfanin ya mika wadannan makudan kudade ga Rasha wadda zata ci gajiyar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.