Biden ya gargadi China a kan illolin taimaka wa Rasha a yakinta da Ukraine
Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi takwaransa na China Xi Jinping a kan illolin taimaka wa Rasha a yakin da take da Ukraine, a yayin da Chinar har yanzu bata nuna alamun bin sahun sauran kasashen duniya wajen yin Allah wadai da Rasha ba.
Wallafawa ranar:
Fadar White House ta ce Biden ya yi wa shugaba Xi bayani ne a game da rashin alfanun taimaka wa Rasha da kayayyakin yaki a yayin da take yin dirar mikiya a kan biranen Ukraine da fararen hula.
Sanarwar Fadar gwamnatin Amurka na zuwa ne bayan ganawa ta sa’o’i biyu da shugabannin suka yi ta wayar tarho a jiya Juma’a.
Sai dai China ba ta bayyana takamammen matsayinta ba bayan ganawar, inda tashar talabijin kasar ta ruwaito shugaba Xi yana cewa, babu abin da wanna yaki zai tsainana wa kowa, ayayin da babu wani bayani a game da caccakar Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu