Yakin Rasha da Ukraine ya maida yara fiye da miliyan 1 'yan gudun hijira
Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu yara kanana kimanin miliyan 1 da dubu 400 ne suka tsere daga Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki kan kasar da Rasha ta yi a ranar 24 ga watan Fabarairu.
Wallafawa ranar:
Sabon rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM ta fitar a wannan Talata ya nuna cewar fiye da mutane miliyan 3 ne suka tsere daga Ukraine kuma kusan rabinsu kananan yara ne.
Kakakin hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF James Elder, ya shaida wa manema labarai a a birnin Geneva cewa, a kowace rana cikin kwanaki 20 da suka wuce a Ukraine, fiye da yara 70,000 ne ke zama 'yan gudun hijira.
A takaice dai kididdiga ta nuna cewar yaro daya ke zama dan gudun hijira duk bayan dakika 1.
Elder ya kuma jaddada cewa yakin na Rasha da Ukraine na cigaba da kazancewa tare da munanan yanayin da dubban miliyoyin mutane ke rayuwa ta hanyar tagayyara su, tashin hankalin da rabon da a ga irinsa tun yakin duniya na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu