Faustin-Archange Touadéra na shirin yiwa kudin tsarin mulki gyaran fuska
A jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yanzu haka ana cece-kuce biyo bayan bukatar Shugaban kasar na yiwa kudin tsarin mulkin kasar gyara,Faustin Arkange Touadéra ya gabatarwa 'yan Majalisar dokokin kasar da shirin na sa watan da ya gabata.
Wallafawa ranar:
‘Yan adawa da kungiyoyin farar hula sun yi watsi da shirin da suka ce majalisar wakilai basu da hurumi sai dai ta hanyar kuri’ar raba gardama. Inda ma tuni suka bukaci yayi murabus.
Wasu daga cikin jam’iyyoyin siyasa a kasar sun kalubalanci wannan tsarin da Shugaban kasar ke shirin aiwartar da shi ,sun bayyana cewa yin haka tamkar yiwa dimokuradiyya tarkade ne.
Kasar tsawon shekaru ta fuskanci rigigimu na siyasa da suka janyo juyin mulki tareda hadasa yaki tsakanin kabilu wannan kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu