Isa ga babban shafi

Human Rights ta yi Allah wadai da take hakkin dan Adama a Burundi

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce hukumomin tsaron Burundi sun ci zarafin mutanen da ake zargi da kasancewa 'yan jam'iyyun adawa ne ko kuma suna aiki da kungiyoyin 'yan adawa masu dauke da makamai.

Zanga-zangar adawa da tsohon shugaban Burundi marigayi Pierre Nkrunziza a shekarar 2015.
Zanga-zangar adawa da tsohon shugaban Burundi marigayi Pierre Nkrunziza a shekarar 2015. © REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

A wani rahoto da ta fitar a ranar Laraba, kungiyar kare hakkin bil adama da ke Amurka ta ce jami’an leken asiri na kasa, da ‘yan sanda, da kuma wakilan matasan jam’iyyar da ke mulki, sun mayar da martani kan hare-haren da aka kai kan fararen hula da jami’an gwamnati a kasar ta hanyar daukar matakai masu tsanani.

Human Rights Watch ta ce hukumomi kasar Burundi sun nuna rashin kulawa ga sahihin bincike, da kuma tattara shaidu na hakika, ko kuma aiwatar da tsarin da ya dace don hukunta wadanda ke da alhakin kai harin.

Kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta kara da cewar ta yi hira da mutane sama da 30, da suka hada da wadanda abin ya shafa da kuma shaidun cin zarafin da aka aikata, da 'yan uwa, da wakilan jam'iyyar adawa, da kuma masu fafutukar kare hakkin bil'adama na Burundi tsakanin watan Oktoban shekarar 2021 da Afrilun shekarar 2022.

Kungiyar ta kuma sanar da yin nazari tare da tabbatar da faifan bidiyo da ke nuna jami’an sojoji da ‘yan sanda da dama na amincewa da aikata kisan gilla tare da yin nazari kan rahotannin kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin gida da na waje, da rahotannin kafafen yada labarai, da jawaban jami’an gwamnati, da shafukan sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.