Isa ga babban shafi
Burundi

An yi wa mutane 348 kisan gilla a Burundi

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce akalla mutane 348 aka yi wa kisan gilla a rikicin kasar Burundi tsakanin watan Afrilun 2015. Rahoton ya daura laifin kisan akan Jami’an tsaro da ke biyayya ga jam’iyya mai mulkin kasar.

Ana zargin Jami'an tsaro da murkushe 'Yan adawa a Burundi
Ana zargin Jami'an tsaro da murkushe 'Yan adawa a Burundi STRINGER / cds / AFP
Talla

Ofishin kare hakkin bil’adama ne na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da rahoton.

Rahoton ya daura lafin kisan akan ‘Yan sanda da jami’an kwantar da tarzoma da wasu ‘yan sa-kai masu biyayya ga jam’iyyar shugaba Pierre Nkurunziza.

Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zaid Ra’ad Al Hussain ya shaidawa babban taron keta hakkin bil’adama a Geneva irin girman yadda aka ci zarafin bil’adama da keta hakkinsu a Burundi.

Sai dai kuma rahoton ya zargi wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da ke adawa da gwamnatin Nkunziza da kisan mutane 134.

Burundi dai ta fada cikin rikici ne tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkunruziza ya ayyana kudirinsa na yin wa’adin shugabanci na uku, wanda kuma ya zarce a watan Yulin bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.