Isa ga babban shafi
Burundi

An kori dalibai a Burundi saboda shugaban kasa

Wata makarantar sakandare da ke kasar Burundi ta kori yara dalibai 230 saboda sun bata hotan shugaban kasar Pierre Nkurunziza da ke jikin litattafan karatunsu.

An kori daliban wata makaranta a Burundi saboda sun bata hoton shugaban kasar da ke jikin littattafansu na karatu
An kori daliban wata makaranta a Burundi saboda sun bata hoton shugaban kasar da ke jikin littattafansu na karatu AFP PHOTO/Diatezua HANNAH
Talla

Kwizera Guillaume, daraktan ilimi na yankin Ruyigi da ke da nisan kilomita 200 daga Bujumbura ya ce, sun kori yawan daliban da suka kai azuzuwa hudu da ke gudanar da jarabawa.

Kafin wannan, a kwanakin baya akwai wata makarantar da ita ma ta kori dalibai 300 da suka aikata irin wannan laifi a Bujumbura.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.