Isa ga babban shafi
Burundi

Dan adawan kasar Burundi na samun sauki bayan harbin shi a Fuska

A Burundi, rahotanni na cewa mutumin nan mai fafutukar kare hakkin bil’adama da wani dan bindiga ya harba a fuska, na can yana jinya a asibitin birnin Bujumbura, kuma ‘yan uwansa sun ce yana samun sauki.

Pierre-Claver Mbonimpa.
Pierre-Claver Mbonimpa. Martin Ennals Award / capture d'écran
Talla

Pierre-Claver Mbonimpa, na daya daga cikin mutanen da suka fito fili suka nuna adawa da sake tsayawa takara na shugaba Pierre Nkurunziza a zaben da ya gabata

An  dai harbe Mbonimpa da bindiga ne a marecen jiya akan hanyarsa ta komawa gida daga aiki, kwana daya bayan kashe tsohon babban kwamandan askarawan kasar kuma na hannun damar shugaba Nkurunziza, Adolphe Nshimirimana.

Ana dai ci gaba da kai harin sari ka noke a cikin kasar tun bayan kamalla zaben da aka gudanar ba tare da halartar jama'iyar adawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.