Isa ga babban shafi
Burundi

An yi wa Dan jaridar RFI duka a Burundi

Jami’an tsaron kasar Burundi sun kama tare da tsare wakilin rediyo Faransa RFI a birnin Bujumbura Erdras Ndikumana har na tsawon sa’o’i biyu, sannan kuma suka yi masa dukan tsiya har aka kwantar da shi a asibiti.

Esdras Ndikumana Dan jaridar RFI da ya sha duka a Burundi
Esdras Ndikumana Dan jaridar RFI da ya sha duka a Burundi DR
Talla

Lamarin dai ya faru ne lokacin da Ndikumana ya je bincika wani labari kan kisan da aka yi wa janar Adolohe a birnin Bujumbura.

A karshen mako ne aka kashe babban Janar din sojin Burundi, kuma na hannu daman Shugaban kasar Pierre Nkurunziza a wani harin rokoki da aka kai a birnin Bujumbura. Lamarin da a yanzu ke dada haifar da tsoron sake samun barkewar rikici a kasar.

Dan Jaridar da ke kuma aiki da kamfanin dillacin Laraban Faransa ya sha duka ne a lokacin da ya ke aikin daukar hoto a inda aka kai harin a Bujumbura.

Hukumomin RFI da AFP sun bukaci Karin bayani daga mahukuntan Burundi kan dalilin kamawa tare da yi wa ma’aikacinsu duka a kasar.

Tuni dai Burundi ke haramtawa ‘yan jarida da ke aiki a kafofin yada labaran kasashen waje shiga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.