Isa ga babban shafi
Kenya - zimbabwe

Kenyata ya bukaci kasashen Yamma su cirewa Zimbabwe takunkumai

Shugaban Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya yi kira ga kasashen Yammacin Duniya da su kawo karshen takunkuman karya tattalin arziki da suka kakaba wa Zimbabwe.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Kenyatta ya yi wannan kira ne a lokacin da yake karbar bakuncin takwaransa na Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, wanda ya kai ziyarar aikin kwanaki biyu a kasar ta Kenya.

Muna jaddada cewa za mu ci gaba da kokarin ganin cewa an cire wa Zimbabwe takunkuman da aka kakaba mata ba a kan ka’ida ba, takunkuman da ke ci gaba da haddasa mummunar ill aga tattalin arziki da kuma rayuwar al’ummar Zimbabwe.

Shugaban Kenya ya ci gaba da cewa: Wadannan takunkumai ne da kowa ya tabbatar da cewa ba hujjar ci gaba da lafta wa kasar su, domin ba abin da suke haifar wa face kara jefa jama’a a cikin kunci.

Shugaban ya kara da cewa: Saboda haka muna ci gaba da kira ga kasashen yammacin duniya da su cire wadannan takunkumai na rashin adalci.

Mai girma shugaban kasa, ina amfani da wannan dama don jaddada maka cewa, har kullum kasata na shirye don ci gaba da karfafa alaka a tsakaninsu, da kuma shimfida irin wannan hulda da sauran kasashe na Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.