MDD ta yi tayin shiga tsakani don sansanta rikicin siyasar Libya
Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a Libya mai fama da rikici ta yi tayin shiga tsakani don sansanta rikicin siyasar da ya kunno kai tsakanin bangarorin biyu a kasar, bayan da aka samu kafuwar gwamnatoci guda 2 da suka fara gudanar da mulki a baya bayan nan.
Wallafawa ranar:
Kiran na Stephanie Williams ya zo ne kwana guda bayan da majalisar dokokin Libya da ke gabashin kasar ta rantsar da sabon firaminista da nufin maye gurbin mai ci Abdulhamid Dbeibah, matakin da masu lura da al'amura ke fargabar zai iya jefa Libya cikin wani sabon rikici.
Cikin wasu jerin sakwanni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Williams wadda take mashawarciya ta musamman ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kan kasar Libya, ta yi gargadin cewa kafa gwamnatoci biyu masu adawa da juna ba shi ne matakin da zai warware matsalar kasar ba.
Jami’ar ta bukaci Majalisar Wakilai da ke gabashin kasar da kuma Majalisar zartaswa mai hedikwata a birnin Tripoli, da su zabi wakilai shida kowannen su, don kafa kwamitin hadin gwiwa domin samar da matsaya kan sansanta rikicin siyasar da ka iya kazancewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu