Isa ga babban shafi
Libya

Wasu tsageru sun kai wa ministocin Libya hari

‘Yan tada kayar baya sun far wa zaman majalisar ministocin kasar Libya, lamarin da ya haddasa tashin hankalin da ya sanya sai da aka fitar da shugaban kasar daga zauren taron.

Wasu masu tayar da kayar baya a Libya
Wasu masu tayar da kayar baya a Libya REUTERS/Stringer
Talla

Bayan wannan lamari dai, masu tada kayar bayan sun kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen hana gudanar da zabe a kasar.

Bayanai sun ce, an fara ganin alamun rashin tabbas a zagayen fadar shugaban kasar, abin da ya sanya aka baza jami’an tsaro don dakatar da duk wani hari da aka iya aukuwa.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin kasar game  da faruwar lamarin.

Libya dai ta dade cikin tashin hankalin da ke da nasaba da shirye-shiryen zaben kasar, da ya janyo rikicin baya-bayan nan.

A farkon makon da muke ciki ma, sai da rikicin ya yi tsamarin da sai da gwamnatin kasar ta aike da sojoji wasu yankuna don kwantar da tarzoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.