Isa ga babban shafi
Libya

Al'ummar Libya na bikin tunawa da kawo karshen mulkin marigayi Gaddafi

A wannan Alhamis al’ummar Libya ke bikin tunawa da juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba Muammar Gaddafi shekaru 11 da suka wuce, sai dai har yanzu dimokaradiyyar da suke fata bata samu ba, a yayin da wasu ke fargabar dawowar rikici.

Wasu 'yan kasar Libya yayin bikin tunawa da juyin-juya halin kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba marigayi Mu'ammar Gaddafi.
Wasu 'yan kasar Libya yayin bikin tunawa da juyin-juya halin kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba marigayi Mu'ammar Gaddafi. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Libya na cika shekaru 11 da wannan al’amari da ya kawo karshen mulkin shugabanta, Muammar Gaddafi, tare da sanadin barin sa duniya ne a daidai lokacin da kasar da ta shafe shekaru tana fama da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar gabashi da yammacin kasar ta samu firaminista 2 masu hamayya da juna a lokaci guda, wadanda ke zaune a babban birnin kasar Tripoli.

Makonni bayan da majalisar dokoki da ke zaune a yankin gabashin kasar ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Disamba ne ta kada kuri’ar amincewa da nadin  tsohon ministan cikin gida Fathi Bashgha don ya  maye gurbin gwamnatin hadin kan kasa ta wucin gadi, amma Firamisnita mai barin gado, Abdulhamid Dbeibah, ya ce ba zai yiwu ba.

A wannan rana, an kawata babban birnin kasar, Tripoli da tutoci masu kalolin ja, baki da shudi da aka amince da su bayan faduwar Gaddafi.

An shirya gudanar da kade-kade, raye-raye da wasan tirtsitsin wuta a Juma’a, kwana guda bayan cika shekaru 11, a dandalin   shahidai na Tripoli, inda marigayi Gaddafi ya gabatar da wani jawabin neman dauki, kafin juyin juye halin ya ritsa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.