Isa ga babban shafi
Libya

Kasar Libya ta samu kanta da Firaminista guda biyu

Kasar Libya ta samu kanta da Firaminista guda biyu a wannan Alhamis, bayan da majalisar dokokin kasar ta bayyana dan takarar da zai maye gurbin shugaban gwamnatin hadin kan kasa mai ci Abdulhamid Dbeibah, matakin da ya zama barazana ta fuskar haifar da rikici kan kokarin darewa madafun iko.

Sabon Firaministan Libya ta majalisar kasar ta nada Fathi Bashagha.
Sabon Firaministan Libya ta majalisar kasar ta nada Fathi Bashagha. © Zoubeir Souissi, Reuters
Talla

Majalisar wakilan Libya da ke da hedikwata a gabashin kasar ce ta kada kuri’ar amincewa da Fathi Bashagha a matsayin sabon Firaministan da zai shugabanci gwamnatin hadin kai kamar yadda kakakin majalisar Abdullah Bliheg ya tabbatar.

Matakin dai ya yi barazanar zurfafa takaddamar da jagororin siyasar Libya ke yi kan neman madafun iko tsakanin majalisar kasar dake zamanta a gabashi da kuma gwamnatin Firaminista Dbeibah da ke yammacin Libyan a Tripoli babban birnin kasar, inda kwararru suka yi gargadin cewa za a iya samun tashin hankali, sakamakon kin saukar da Firaministan mai ci, duk da sanar da zabar wanda zai maye gurbinsa.

Hakan ya zo ne sa’o’i bayan da kafafen yada labaran Libya suka fitar da rahotannin cewa an budewa motar Dbeibah wuta cikin dare, ba tare da an tantance ko yana cikin motar a lokacin ba.

Sai dai baya bayan nan Majalisar Dinkin Duniya ta hannun kakakinta Stephane Dujarric ta bayyana cewar za ta cigaba da goyon bayan shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya wato Firaminista Abdulhamid Dbeibah, wanda majalisar wakilai ta sanar da nada Fathi Bashagha a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.