Isa ga babban shafi
ZABEN LIBYA

Shugabannin duniya sun yi kashedi dangane da zaben Libya

Manyan Kasashen duniya sun bukaci Libya da ta shirya karbaben zaben da duniya zata amince da shi daga ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa, kamar yadda ta tsara yadda za’a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'Yan majalisu.

Shugabannin kasashen duniya da suka halarci taron taimakawa kasar Libya a Paris
Shugabannin kasashen duniya da suka halarci taron taimakawa kasar Libya a Paris © Niger Presidency
Talla

Bayan wani taro da ya kunshi wasu shugabannin kasashen duniya, a karkashin jagorancin shugaba Emmanuel Macron na Faransa da mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris da kuma shugabannin kasashen dake makotaka da Libya, shugabannin sun yi barazanar saka takunkumi akan duk wani mutum ko wata kasa ko kuma kungiyar da ta nemi yin zagon kasa ga shirin zaben wanda yake da matukar muhimmanci wajen mayar da kasar turbar dimokiradiya.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed dake halartar taron Libya a Faransa tare da shugaba Emmanuel Macron
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed dake halartar taron Libya a Faransa tare da shugaba Emmanuel Macron © Niger Presidency

Sanarwar ta bukaci duk masu ruwa da tsaki a Libya da su sanya hannu wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun zagon kasa ba.

Taron ya gargadi bangarorin dake neman hana ruwa gudu a ciki da wajen kasar da su kwan da sanin cewar za’a dauki mataki akan su muddin suka yi katsalandan.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci bangarorin siyasar kasar da su shiga a dama da su wajen zaben shugaban kasar da kuma na Yan majalisu, wanda ya bayyana shi a matsayin matakin farko na tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar.

A sakon da ya aikewa taron ta bidiyo, Guterres ya kuma bukace su da su amince da tsarin da kuma sakamakon zaben da za’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.