Isa ga babban shafi

Majalisar rikon kwaryar Libya ta dakatar da ministan harkokin waje

Majalisar rikon kwaryar kasar Libya ta dakatar da Ministar harkokin wajen kasar Najila Al Mangoush daga mukamin ta, biyo bayan zargin daukar wasu matakai ba tare da ta samu amincewar ta ba. 

Tsohuwar Ministar harakokin wajen Libya Najla al-Mangoush tareda Ministan harakokin wajen Turkiya a Tripoli
Tsohuwar Ministar harakokin wajen Libya Najla al-Mangoush tareda Ministan harakokin wajen Turkiya a Tripoli AFP - MAHMUD TURKIA
Talla

Matakin dakatar da wannan jami’ar diflomasiyar na zuwa ne yayin da suka rage kasa da mako guda a gudanar da  babban taro dangane da makomar kasar ta Libya.

Ministar harakokin wajen Libya  Najla Mangoush
Ministar harakokin wajen Libya Najla Mangoush AFP - RYAD KRAMDI

Majalisar rikon kwaryar kasar ta kaddamar da bincike don tattance gaskiyar tuhumar da ake yiwa Najla AlMangoush, inda wata majiya ke nuna cewa  kalaman ta na bayyana aniyar hukumomin Libya na tattaunawa da Amurka domin tasa keyar daya daga cikin mutanen da ake zargin yana da hannun a harin jirgin saman Lockerbie. 

Hukumomin Libya sun haramtawa Mangoush izinin fita daga kasar yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.