Isa ga babban shafi
Nijar - Libya

MDD ta kwashe 'yan gudun hijira 172 daga Libya zuwa Nijar

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta sanar da kwashe masu neman mafaka ko 'yan gudun hijira 172 daga inda ake tsare da su a Libya zuwa Jamhuriyar Nijar.

Baki sun yi jerin gwano don karbar abinci da hukumar UNHCR ta raba, sakamakon barkewar cutar Coronavirus a Tripoli, Libya 12 ga Mayu, 2020.
Baki sun yi jerin gwano don karbar abinci da hukumar UNHCR ta raba, sakamakon barkewar cutar Coronavirus a Tripoli, Libya 12 ga Mayu, 2020. © REUTERS/Ayman Al-Sahili/Hoton Fayil
Talla

Karo na farko kenan da irin wannan aikin jigila ya gudana cikin sama da shekara guda.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta UNHCR ta fitar ta ce da yawa daga cikin wadanda ta kwashe din an tsare su ne a cikin mawuyacin hali a kasar Libya.

Mutanen da aka kubutar dai sun hada da iyalai, da yaran dake tafiya su kadai, har ma da wani jariri da aka haifa makwanni kadan da suka gabata.

Tun shekarar 2011 kasar Libya ta fada cikin rudani da rikici bayan hambarar da gwamnatin Mu’ammar Gaddhafi a shekara ta 2011, inda ta zama mashigar da ‘yan ci rani ke amfani da ita wajen kokarin ketarawa nahiyar Turai.

Sai dai da yawa daga cikin ‘yan ci ranin ana tsare su ne cikin wani yanayi da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi Allah wadai da su.

A cikin watan Oktoban da ya gabata hukumomin kasar Libya suka janye dokar hana jiragen kwashe ‘yan ci ranin fita daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.