Isa ga babban shafi
Nijar-Hijira

Nijar ta bai wa 'yan gudun hijira takardar zama 'yan kasa

Bayan shafe kusan shekaru hudu da soma karbar 'yan gudun hijira daga kasashen gabashi da kuma yammacin nahiyar Afrika,  yanzu haka Jamuhuriya Nijar ta bai wa fiye da rabin adadinsu  'yancin zama a kasar. Wannan shi zai kawo karshen  zaman jiran-tsammani da 'yan gudun hijirar akalla dubu 1 da 200 suka shafe tsawon lokaci suna yi a sansaninsu da ke yankin Agadas a arewacin kasar.

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016.
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Omar Sanni daga Agadez

 

02:51

Nijar ta bai wa 'yan gudun hijira takardar zama 'yan kasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.