Isa ga babban shafi
Mozambique - Ta'addanci

Dakarun Rwanda sun fatattaki 'yan ta'adda a Mozambique

Sojojin Ruwanda da aka tura zuwa Mozambique don taimakawa dakarun kasar wajen yakar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, sun sanar da sake kwace iko da birnin Mocimboa da Praia mai babbar tashar jiragen ruwa da ke arewacin kasar daga hannun masu tsattsauran ra'ayin.

Dakarun Rwanda da ke taimakawa na Mozambique wajen yaki da 'yan ta'adda.
Dakarun Rwanda da ke taimakawa na Mozambique wajen yaki da 'yan ta'adda. REUTERS - JEAN BIZIMANA
Talla

Kafin nasarar ta jami'an tsaron Rwanda da Mozambique dai birnin Mocimboa ya kasance babban sansanin masu tayar da kayar baya tsawon fiye da shekaru biyu.

Kakakin rundunar sojin Ruwanda Kanal Ronald Rwivanga ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP samun nasarar inda ya ce tabbas Mocimboa da Praia ya fadi.

A garin mai katafariyar tashar jiragen ruwa, ne dai mayakan da ke kiransu da ‘yan Al Shebaab masu alaka da IS, suka fara kaddamar da hare-hare a watan Oktoban 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.