Sojojin Rwanda dubu 1 sun isa kasar Mozambique don yaki da ta'addanci
Rwanda ta aikewa Mozambique taimakon dakarun Soji na musamman dubu guda don taimaka mata yaki da hare-haren ta’addanci da ke ci gaba da tsananta a yankin arewacin kasar mai arzikin iskar gas.
Wallafawa ranar:
Tun farko Mozambique da kanta ta nemi taimakon dakarun daga makwabtanta bayan da hare-haren mayakan masu ikirarin jihadi ya hallaka mutane dubu 2 tare da raba wasu fiye da dubu 700 da muhallansu.
Ma’aikatar tsaron Rwanda ta bakin kakakinta Lonard Rwivanga ta ce baya ga dakarun dubu guda akwai kuma tallafin tsabar kudi dala miliyan 12 daga kasashen yankin 16 da ke karkashin kungiyar SADC mai rajin tabbatar da ci gaban kasashen yankin kudancin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu