Isa ga babban shafi
Rwanda - Mozambique

Rwanda zata tura sojoji 1000 don taimakawa Mozambique

Kasar Rwanda ta bayyana shirin tura sojojinta dubu daya zuwa kasar Mozambique, domin taimaka wa kasar yaki da ‘yan ta’adda a lardin Cabo Delgado.

Sojojin Rwanda a yankin Jomba na Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ranar 24 ga watan Janairu 20009.
Sojojin Rwanda a yankin Jomba na Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ranar 24 ga watan Janairu 20009. © Photo AFP / Lionel Healing
Talla

Rwanda ta amince ta tura sojojin ne bayan da taron shugabannin kasashen yankin kudancin Afrika karkashin inuwar kungiyarsu ta SADC ta bukaci a taimaka wa kasar don murkushe ‘yan ta’addan.

Daga shekarar 2017 zuwa farkon wannan shekara, fadan da aka gwabzawa a yankin na Cabo Delgado, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu biyu da 900 tare da tilasta wa sama da dubu 800 barin gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.