Isa ga babban shafi
Amurka - Afirka

Amurka ta sanya jagororin masu ikirarin jihadi 5 cikin bakin kundinta

Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya sunayen wasu mutane 5 cikin bakin kundinta na jerin ‘yan ta’adda, kasancewarsu jagororin kungiyoyi masu ikirarin jihadi a Afirka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. KEN CEDENO POOL/AFP
Talla

Hakan na nufin Amurkan ta kwace duk wata kadara ko muradunsu da ke karkashin ikonta.

Cikin sanarwar da ya fitar a jiya, sakataren harkokin waje Antony Blinken, ya ce wadan suka shiga bakin kundin sun hada da, babban kwamandan kungiyar IS a Mozambique Bonomade Machude Omar, da ya jagoranci mummunan harin da aka kai kan garin Palma a watan Maris.

Sauran mutanen sun hada da Sidan ag Hitta, da Salem ould Breihmatt, manyan shugabannin kungiyar Jama'at Nasr al-Islam wal Muslimin (JNIM) ta Al-Qaeda reshen Mali.

Sai kuma Ali Mohamed Rage, mai magana da yawun kungiyar masu tsattsauran ra'ayi na Al-Shabaab, da Abdikadir Mohamed Abdikadir, mai tsara ayyukan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.